Dakarun Najeriya na da cikakkiyar ƙwarewar kawar da ta'addanci - Kaftin Bakoji
06 February 2026

Dakarun Najeriya na da cikakkiyar ƙwarewar kawar da ta'addanci - Kaftin Bakoji

Bakonmu a Yau

About

Babban Sifeton Ƴansandan Najeriya Kayode Egbetokun, ya aike runduna ta musamman domin mara wa sojoji baya wajen tabbatar da tsaro a ƙaramar hukumar Kaiama da ke jihar Kwara, inda ‘yan ta’adda suka salwantar da rayukan mutane kusan 170.

Yanzu haka dai ana dakon ganin tasirin matakan da haɗin gwiwar jami’an tsaron Najeriyar zai yi wajen murƙushe matsalar tsaron da ke daɗa ƙamari, lamarin da ke ta’azzara duk da jerin farmakin da jami’an tsaro ke kaiwa, tare da tarwatsa sansanonin ‘yan ta’adda a sassan arewacin ƙasar.

Kan wannan lamari Nura Ado Suleiman ya tattauna da Kaftin Abdullahi Bakoji mai ritaya masanin tsaro a Najeriya.