About
An shiga rana ta uku a ci gaba da gudanar da Babban Taron Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81, wanda ke matsayin dama ga illahirn shugabannin ƙasashe don gabatar da jawabai kan batutuwan da suka shafi duniya.
To sai dai tun a ranar farko da aka buɗe wannan zama, shugaban Amurka Donald Trump ya fito fili inda ya yi fatali da wasu batutuwa da suka shafi ƙasa da ƙasa. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da masani diflomasiyya Ambasada Sulaiman Dahiru, domin yi dubi a game da muhimmancin wannan zama da ake yi kowane watan Satumba.