
About
Har yanzu ana ci gaba da zaman ɗar-ɗar a ƙasar Kamaru sakamakon tashin hankalin da ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasar da aka bayyana shugaba Paul Biya a matsayin wanda ya samu nasara.
Shugaban 'yan adawa Issa Tchiroma Bakary da ya zo na biyu ya ƙi amincewa da sakamakon, inda ya buƙaci jama'a da su sake fitowa zanga zanga a ranakun litinin da Talata da kuma Laraba na makon gobe, yayin da a ɓangare ɗaya gwamnati ke barazanar ladabtar da duk wanda ya saɓa dokokin ƙasar, ciki harda shi Isa Tchiroma.
Domin tattauna halin da ake ciki a ƙasar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon Jakadan Kamaru a Faransa, Ambasada Muhammadu Sani.
Ku alatsa alamar sauti don sauraren tattaunawarsu...