
07 May 2026
Ambasada Kazaure kan kiran wasu ƴanmajalisar Najeriya na kwace lasisin MTN da DSTV
Bakonmu a Yau
About
Wasu daga cikin Ƴan Majalisun Dattawan Najeriya sun buƙaci ɗaukar matakai maus tsauri a kan Afirka ta Kudu, ciki harda kwace lasisin kamfanonin su na MTN da DSTV saboda yadda ake kai wa ƴan ƙasar hari ake kuma kashe su.
Majalisar ta yanke hukuncin tura tawaga Afirka ta Kudu domin tattaunawa da hukumomin ƙasar, yayin da shi ma bangaren gwamnati ya tura ministan harkokin waje. Ambasada Ibrahim Kazaure, tsohon Jakadan Najeriya a Saudi Arabia ya yi tsokaci a kai, a tattaunawar su da Bashir Ibrahim Idris.