Alhaji Muhammed Sani Zoro tsohon shugaban NUJ kan ranar ƴan jarida ta duniya
04 May 2026

Alhaji Muhammed Sani Zoro tsohon shugaban NUJ kan ranar ƴan jarida ta duniya

Bakonmu a Yau

About

Kamar dai kowace shekara, 3 ga watan Mayu ita ce ranar kare ƴancin aikin yaɗa labarai a duniya, inda rahotannin da ƙungiyoyin da ke fafutuka a wannan fage ke nuni da cewa an samu gagarumin koma-baya ta fannin aikin jarida a cikin shekarar da ta gabata.

Dangane da wannan rana, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da tsohon shugaban ƙungiyar Ƴan Jarida ta Najeriya (NUJ) Honnorable Alhaji Muhammed Sani Zoro, wanda da farko ya fara yin tsokaci a game da irin sauye-sauyen da aka samu a aikin jarida saboda dalilai masu nasaba da zamani.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.