AbdulHakim Garba Funtua kan Kwamitin Zaman Lafiya Gaza da Trump ya kafa
20 February 2026

AbdulHakim Garba Funtua kan Kwamitin Zaman Lafiya Gaza da Trump ya kafa

Bakonmu a Yau

About

A ranar Alhamis, shugaban Amurka Donald Trump ya ƙaddamar da fara aikin  Kwamitin Zaman Lafiyar Duniya da ya kafa.

Wakilai daga aƙalla ƙasashe 47 da kuma ƙungiyar Tarayyar Turai da Isra’ila ne suka halarci taron farkon na Kwamitin Zaman Lafiyar na Duniya a birnin Washington.

Muhimman batutuwan da taron ya mayar da hankali kai sun haɗa da kafa Rundunar zaman lafiya a Gaza, da karɓe makamai daga hannun Hamas, da kuma sake gina Zirin na Gaza.

Shiga alamar sauti, domin sauraron tattaunawar Nura Ado Suleiman da AbdulHakim Garba Funtua, masanin siyasar ƙasa da ƙasa.