
About
Shirin "Al'adunmu na gado" a wannan makon tare da Nura Ado Suleiman ya leƙa ne Masarautar Hausawa da ke nahiyar Turai, inda a makon Masarautar ta karɓi baƙuncin Mai Martaba Sarkin Daura Dakta Umar Faruk Umar da ya yi tattaki daga Tarayyar Najeriya, domin halartar bikin karrama Sarkin Hausawan na Turai da kuma naɗin wasu sabbin muƙaman na sarauta da suka shafi sassan nahiyar.
Daya daga cikin kalubalen da Hausawa mazauna Turai ke fuskanta, shi ne bacewar harshen Hausa da al’adu a tsakaninsu, sai dai a yayin ziyarar da ya kai wa Sarkin Hausawan Turai da ke birnin Paris Alhaji Surajo Jan Kaɗo, Mai Martaba Sarkin Daura Dakta Umar Faruk Umar, ya yi alkawarin farfaɗo da martabar harshen na Hausa.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.